Tatsuniya wani ƙagaggen labari ne da iyaye da kakanni suke amfani dashi wajen aika saƙo da gina tarbiyyar ƙananan yara. A al’adance anfi yin tatsuniya da daddare, bayan anci abincin dare. A irin wannan lokacinne ‘yanmata da samari kan tafi dandali su kuma yara kanyi tatsuniyoyi da wasanni a cikin gida.
Duk da dai mafi yawan labarin dake ciki ba gaskiya bane, su kansa mutum lulawa duniyar tunani, ya dinga gani kamar gaske; su dodo, gizo da ƙoƙi, kogin madara, gonar nama, budurwar danƙo dadaisauransu. A yarinta, kowa a cikin sa’o’insa akwai tatsuniyar da ya fiso, wanda da an zauna za’ai tatsuniya ita zai bayar, baya gajiya da maimaitata. Tatsuniyar gizo da ƙoƙi ita tafi shahara, akwai ɗan ƙashin gwiwa, saniya mai magana, takitse, shaida, Nagoma, daskindariɗi dadaisauransu. Duk waɗannan saƙonni suke isarwa akan sha’ani na zamantakewa; bin na gaba, biyayya ga iyaye, rashin tasirin asiri, ƙarshen ƙarya, ƙarshen ƙwadayi da makamantansu.
A misali, labarin dake cikin tatsuniyar Nagoma yayi nuni akan illar ƙarya da ha’inci, cin amana da kuma ƙarshen me yinsu. Nagoma ya kasance babba a cikin gidansu, yana da ƙannai tara, mahaifinsu maharbi ne. Kullum yaje harbi ya dawo da tsuntsun daya harbo sai nagoma ya ɗauka ya gasa ya cinye shi kadai, kullum haka, in an tambaya sai kowa yave bashi bane, da abin ya ishi mahaifinsu sai yace aje kogin rantsuwa. Na ɗaya ya shiga yayi rantsuwa da waƙa:
Ni na ɗaya na ɗayan babaye,
In ni naci tsuntsun babaye,
Ruwa tafi dani, kar ka dawo dani.
A haka har aka zo kan nagoma, aikuwa ruwa ya tafi dashi, yanuwansa da mahaifinsa sukaita kuka da baƙin ciƙin rabuwa dashi. Ruwa yakai nagoma bakin ruwa wajen wata dodanniya, yana ta kuka ya roƙi dodanniya kar ta cinye shi, ta haƙura ta mayar dashi ɗan ta, ta siya masa doki yana zuwa gari yana mata tallan ƙosai. Bayan shekaru, watarana yana tafiya sai yanuwansa suka ganshi, a haka har ya kaisu wajen dodanniya suka roƙeta ta yarda zata bada shi amma sai an bata kayan abinci ɗari da gomiya bakwai, haka kuwa akai. Aka kaiwa dodanniya kwaɗi da ƙwari ta yarda nagoma ya dawo gida cikin yanuwansa da alƙawarin bazai ƙara sata ba.
Burin mu a kullum shine al’adun bahaushe da suke da kyau a farfaɗo dasu, a taimaki yara masu tasowa wajen saita musu tunani da tarbiyya. Duk da dai yanzu fasahar zamani tayi awon gaba da mafi yawa na al’adar, mun zubar da tamu mun ari ta wasu. Allah Ya sa wannan ya zame mana kukan kurciya. Mungode da gyararrakin ku garemu da kuma saƙwannin da kuke turowa, ako dayaushe ƙofarmu a buɗe take: fsaliyuhh@gmail.com.
©fsa2018.
Photo credit: Google