Gyartai

CalabashTree111.JPGGyartai ko Gyattai wata daɗaɗɗiyar sana’ace a ƙasar hausa wadda a wannan zamanin da muke ciki an manta da ita. Duk wani abin da akeyi da ‘duma’ in ya fashe ko ya tsage to gyartai ke ɗinkewa; ƙwarya, kuttu, ludayi, mara, ƙoƙo, masaki dadaisauransu, duk da dai ita gora ba’a ɗinketa kasancewar ruwa ake zubawa a ciki in ta tsage ko ta fashe saidai a haƙura da ita.

Ko a wancan lokacin ƙasƙantacciyar sana’ace, ba’a cika bata ƙima ba. Lokacin da ba’a ganewa amfani da tangaran ko roba ba, da kayan duma ake amfani wajen aikace-aikacen gida. Sana’ar gyartai na daga cikin da daɗaɗɗun sana’o’in da bahaushe yake yi, na zaɓi yin magana akanta ne a saboda tuna mana da da kuma ‘yan baya su amfana. Kasancewar wannan lokacin ma kafin kaga ƙwarya a gadajen mutane ana daɗewa ɗaiɗaiƙu ne ke da ita sai ko masu tallan fura bare har a tuna da wani mai ɗinkinta ko gyaranta.

Ku ma zaku iya faɗin naku ra’ayin ta kan fsaliyuhh@gmail.com ko sashen ajiyar ra’ayi dake ƙasa.

©fsa2018

Photo credit: Google.

Author: bahaushiyaonline

This site is aimed at reviving the forgotten Hausa Culture and Value. It will consist of Random posts in Hausa and English or the mix of both(ingausa). I do hope we benefit from eachother and learn.

One thought on “Gyartai”

Leave a comment